An rufe hukumomin gwamnati a Amurka
October 1, 2013Fadar gwamnatin Amurka ta white house ta bada umurnin tsayar da tafiyar da harkokin gwamnati , sakamakon sabanin da aka samu tsakanin 'yan majalisa, daya jagoranci kin amincewa da kasafin shekara ta 2014 da Obama ya gabatar. Wannan dai shine karon farko da Amurkan ta fuskanci irin wannan yanayi cikin shekaru 17 da suka gabata. Shugaba Obama ya ce babu shakka rufe hukumomin zai shafi tattalin arzikin kasar.
Da misalin karfe tara da rabi agogon Amurkan ne dai, akesaran 'yan majalisar Dottijan kasar za su koma zama, a daidai lokacin da 'yan demokrats zasu yi watsi da gabatarwar 'yan majalisar wakilai na daukar nauyin kula da harkokin gwamnati. Tuni dai 'yan demokrat din suka yi gargadin cewar, tsayar da harkokin gwamnati, zai hana ma'aikata dubu 800 samun albashinsu, kana ya haifar da cikas a kokarin farfado da tattalin kasar.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu