An rataye fursunoni 42 a Iraki
September 25, 2017Talla
Majalisar shura ta kasar Iraki ce ta aiwatar da hukuncin kisan a gidan yarin Nasiriyah da ke kudancin kasar, inda aka baiwa iyalai da sauran dangin mamatan damar zuwa harabar gidan yarin dan ban kwana da yan uwan nasu kafin aiwatar da kisan.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, ta yi Allah wadai da hukuncin kisa ta hanyar rataya da hukumomin Iraki suka zartar a kan fursunonin 42. Amnesty ta ce Iraki ta aiwatar da hukuncin kisa mafi girma baya ga kasashen Chana da Iran da kuma Saudiya.