An rantsar da sabon shugaban Indonesia Prabowo Subianto
October 20, 2024Sabon shugaban kasar Indonesia Prabowo Subianto ya karbi rantsuwar kama aiki yau Lahadi a Jakarta babban birnin kasar, bayan rantse wa da Alkur'ani mai girma a kasar da ta fi kowa yawan musulmi a duniya.
Karin bayani:Indonesiya: Prabowo Subianto ya yi ikrarin lashe zaben shugaban kasa
Mr Prabowo Subianto ya gaji mulkin ne daga hannun shugaba mai barin gado Joko Widodo, kuma an rantsar da shi tare da mataimakinsa Gibran Rakabuming Raka, wanda shi ne tsohon magajin garin Surakarta, kuma babban dan tsohon shugaban kasa mai barin gado Joko Widodo.
karin bayani:Indonesiya ta fuskanci girgizar kasa
Manyan baki daga kaashe sama da 30 ne suka halarci bikin rantsuwar, cikinsu har da mataimakin shugaban China Han Zheng, da jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield, wadda ta wakilci shugaban Amurka Joe Biden, da dai sauran baki daga kasashen duniya.