An rantsar da Kiir na karin shekaru uku | Labarai | DW | 08.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsar da Kiir na karin shekaru uku

Matakin ya biyo bayan dage zaben kasar ne da majalisa ta yi saboda yakin batsatsa da ci-gaban zubar da jini da kasar ke ciki musamman a yankin arewaci.

An rantsar da Salva Kiir a matsayin shugaban Sudan ta Kudu na karin shekaru uku nan gaba. Majalisar dai ta zartar da cewar, Kiir baya bukatar a rantsar da shi a hukumance, kasancewar ya na kan karagar mulki.

Shugaban kasar ya yiwa majalisar alkawarin cewar, zai tattabar da zaman lafiya tare da sasantawa da shugaban tawaye Riek Machar. Fadan neman madafan iko na sojojin bangarorin biyu na tsawon watanni 18 dai, ya yi sanadiyyar dubban rayukan mutane.

A watan Maris da ya gabata ne majalisar dokokin Sudan ta kudu ta sanar da dage gudanar da zaben kasar, wanda ya kamata a gudanar a farkon watan Yuli da muke ciki, tare da kara wa'adin shugaba Kiir, mutumin da ya jagoranci wannan 'yar jaririyar kasar Afirka mai albarkatun man petur, tun samun 'yancinta daga Sudan shekara ta 2011. Sai dai a daya hannun tsohon mataimakinsa Machar, ya zargi Kiir da fadada wa'adin mulkinsa ba bisa ka'ida ba , tare da kalubalantarsa da ya sauka daga mulki.

An rantsar da Salva Kiir ne yini guda kafin bukin cikar kasar shekaru hudu da samun 'yancin kai. Bukukuwan da za su gudana a daidai lokacin da ake cigaba da gwabza fada a yankin arecin kasar mai albarkatun man petur.