An nemi a tsagaita wuta a rikicin Siriya | Labarai | DW | 21.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nemi a tsagaita wuta a rikicin Siriya

Gwamnatin Rasha ta musanta zargin hannu a kisan fararen hula a Siriya tare da yin kira ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya na shirya zama don kawo karshen zubda jini da ke gudana yanzu haka a kasar.

Rahotanni na cewa, dakarun gwamnati sun yi ta luguden wuta a gabashin Ghouta inda aka tabbatar da mutuwar mutane akalla dari biyu da hamsin a sanadiyar sabon farmaki da aka kaddamar a yankin da ya kasance karkashin ikon 'yan tawaye.

Rasha da ke marawa bangaren gwamnatin Bashar al-Assad baya a yakin na Siriya na fiye da shekaru shida ta bukaci a yi zama na musanman kuma cikin gaggawa don lalubo hanyar da za a shawo kan barin wuta da ake ci gaba da yi a kasar.

Dakarun gwamnati da ke kokarin kwace yankin daga hannun 'yan tawayen sun tsananta hare-haren a yankin da shi ne tunga na karshe da ke hannun 'yan tawayen a wajen birnin Damascus. Shugabanin kasashen duniya da kungiyoyi na masu rajin kare hakkin bil'adama sun baiyana halin da ake ciki a matsayin abin takaici da rashin tausayi.

Alkaluma na cewa, mutane fiye da dubu dari hudu suka mutu a sanadiyar rikicin da ya barke a kasar ta Siriya kan neman shugaba Bashar al-Assad ya sauka daga madafun iko.