An nada sabuwar gwamnati a Ivory Coast wato Kodivuwa | Labarai | DW | 16.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nada sabuwar gwamnati a Ivory Coast wato Kodivuwa

Shugaban Ivory Coast wato Kodivuwa, Laurent Ggagbo ya nada sabuwar gwamnatinsa a yau asabar, kwanaki 10 bayan tabargazar wani dati mai guba ta tilastawa ministocin gwamnati yin murabus, amma wasu manyan ministoci sun ci gaba da rike mukamansu. Shugaba Gbagbo ya sake ministocin muhalli da na sufuri wadanda dukkan su suka sha suka bayan jibge sharar mai guba a wurare da dama na birnin Abidjan, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 7 sannan wasu dubbai suka kamu da cututtuka iri daban daban. A kuma halin da ake ciki mujallar Der Spiegel ta nan Jamus ta rawaito cewa za´a komo da sharar mai guba zuwa Turai, inda za´a jibge ta a wani juji na zubar da shara ta musamman a kasar Faransa.