An nada sabon shugaban wucin gadi a Ivory Coast | Labarai | DW | 05.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nada sabon shugaban wucin gadi a Ivory Coast

IVORY COAST

An nada gwamnan babban bankin Afrika ta yamma,Charles Konan Banny,a matsayin prime minista na wucin gadi a kasar Ivory coast.

Wannan nadi da masu shiga tsakani na Afrika suka yi a jiya lahadi, ya samu goyon bayan yan adawa da yan tawayen kasar.

Ana kuma sa ran zai kawo karshen kiki kaka da aka samu a shirin samar da zaman lafiya na kasar ta Ivory Coast.

Karkashin wani shiri dake da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya,Banny yana da ikon kwance damarar yakin yan tawaye tare kuma da yin wasu gyare gyare da suka kamata ga manufofin zabe na kasar,kafin shirya zaben shugaban kasa a watan oktoba na shekara mai zuwa.