An nada sabbin ministoci a Zimbabuwe | Siyasa | DW | 01.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An nada sabbin ministoci a Zimbabuwe

Sabon shugaban kasar Zimbabuwe Emmerson Mnangagwa a wannan Juma'a ya nada manyan jami'an sojin kasar a manyan mukamai na majalisar ministocinsa.

Shi dai Shugaba Emmerson Mnangagwa mai shekaru 75 da aka rantsar mako guda ya wuce bayan murabus din Robert Mugabe mai shekaru 93, ya nada Manjo-Janar Sibusiso Moyo a mukamin ministan harkokin waje, sannan ya ba wa Air Marshall Perence Shiri mukamin ministan noma da raya kasa da ke da muhimmanci a Zimbabuwe.

Sai dai tun ba a kai ko ina ba Shugaba Mnangagwa ya fara shan suka bisa nade-naden da ya yi na majalisar ministocinsa, musamman manyan sojojin da ya ba su mukamai da sake nada wasu kusoshi na tsohuwar gwamnatin Mugabe amma ya mayar da 'yan adawa saniyar ware. Mashaharta da dama sun soki jerin sunayen ministoci, sannan da yawa daga cikin 'yan kasar ta Zimbabuwe sun nuna rashi jin dadinsu. Sai dai a nata bangare gwamnati ta kare wannan zabi da ta yi tana mai cewa ta yi adalci.

Shugaba Mnangagwa dai bai ba da mukami koda guda daya ga bangaren jam'iyyar ZANU-PF da ya nuna goyon baya ga matar Mugabe wato Grace Mugabe ba a yunkurin maye gurbin mijinta ba.

Sauti da bidiyo akan labarin