An nada sabbin mataimakan shugaban Zimbabuwe | Labarai | DW | 10.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nada sabbin mataimakan shugaban Zimbabuwe

Shugaban Zimbabuwe Robert Mugabe ya nada sabbin mataimakan shugaban kasa

Shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe ya nada ministan shari'a na kasar Emmerson Mnangagwa a matsayin sabon mataimakin shugaban kasa.

Mugabe dan shekaru 90 da haihuwa, ya tabbatar da nadin na Emmerson Mnangagwa dan shekaru 68 da haihuwa, bayan ya fatattaki tsohuwar mataimakiyar shugaba Joice Mujuru, wadda kuma ta rasa mukami a jam'iyyar ZANU-PF mai mulki. An nada Mnangagwa tare da Phelekezela Mphoko tsohon jakadan kasar a Afirka ta Kudu wadanda za su rike mukamun na mataimakan shugaban kasar. Shugaba Mugabe ya ce Mnangagwa ke zama mataimakain shugaba na farko.

Ana ci gaba da zama rashin tabbas kan wanda zai gaji mulkin kasar ta Zimbabuwe bayan Robert Mugabe wanda yake mulki tun shekarar 1980, kuma ana rade-radi tsakanin matar shugaban Grace Mugabe da kuma sabon mataimakin shugaban Emmerson Mnangagwa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba