An mika Niragira ga hukumomin Burundi | Labarai | DW | 23.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An mika Niragira ga hukumomin Burundi

Hukumomi a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango sun sako wakilin Deutsche Welle Antediteste Niragira, wanda suka tsare kwanaki biyar din da suka gabata inda suka mika shi ga 'yan sandan Burundi.

Shi dai dan jaridan Antediteste Niragira ya na kan aikin hada rahotanni ne da suka shafi rayuwar 'yan hijira da ke kan iyakar Kwagon da kuma Burundi ne, wanda kuwa jami'an leken asirin kasar suka kama shi. Tashar Deutsche Welle wato DW ta tabbatar da labarin sakin Niragira cikin wata sanarwa. Da fari dai jami'an leken asirin na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwangon sun zargi dan jaridan na Deutsche Welle ne da leken asiri sai dai bayan tambayoyi sun gaza bayar da gamsassun bayanai kan ikirarin da suka yi.