1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An mayar wa jamhuriyar Benin kayayyakin tarihinta

Ramatu Garba Baba
November 11, 2021

Murna da shagulgula al'ummar jamhuriyar Benin suka kwashe yini guda suna yi a sakamakon mayar wa kasar da wasu kayayyakin tarihinta da Faransa ta sace a lokacin mulkin mallaka.

https://p.dw.com/p/42rGe
Benin | Rückkehr von Kunstobjekten in Cotonou
Hoto: Séraphin Zounyekpe

Cikin yanayi na raye-raye da wake-wake al'ummar Jamhuriyar Benin suka karbi wasu daga cikin kayayyakin tarihin kasar da Faransa ta kwashe a lokacin mulkin mallaka, sama da shekaru dari da talatin da suka gabata..

Jama'a daga sassan kasar da suka yi shiga ta al'adun gargajiya, sun mamaye babban birnin kasar suna dakon isowar kayayyakin da aka wuce da su daga filin jirgin saman kasar ya zuwa fadar gwamnatin kasar tare da rakiyan dawakai na alfarma.

Shugaba Patrice Talon a jawabin da yayi ma 'yan kasa, ya baiyana farin cikin da ya ce bai misultuwa, ya ce, rana ce da kowanne dan kasa ke alfahari da ita, ya kuma yi alkwarin ganin an dawo wa jamhuriyyar Benin sauran kayayyakin tarihinta da aka sace. Kasashen Afrika da dama na ci gaba da fafutukar ganin an maido musu da dukiyar kayayyakin tarihi dana al'adu da kasashen da suka yi musu mulkin mallaka suka wawushe a wancan lokacin.