An maido da layukan waya a jihar Borno | Labarai | DW | 19.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An maido da layukan waya a jihar Borno

Rahotanni daga Tarayyar Najeriya na cewa an maido layukan wayoyin salula a garin Maiduguri na jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar wanda ke fama da rikici.

African man on cellphone

Handys in Afrika

Da yake karin haske game da maido da layukan wayar, wani babban jami'in sojin Najeriya da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa ya zuwa yanzu za a takaita wannan sassauci da aka yi ne kawai ga birnin Maiduguri da kewaye.

Mazauna garin na Maiduguri dai sun ce duk da cewar layukan wayar sun fara aiki, amma da wuya idan an buga ake iya samu wayar ta shiga yayin da wasu ke cewar su kan iya yin kira jefi-jefi.

A ranar 15 ga watan Mayun da ya gabata ne dai aka katse sadarwa ta waya a Borno da Yobe da kuma jihar Adamawa bayan da aka kakaba wa jihohin uku dokar ta baci a wani mataki na fatattakar 'yan kungiyar Jama'ati Ahli Sunnah Lida'awati Wal Jihad da aka fi sani da suna Boko Haram daga cikinsu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Halima Balaraba Abbas