An kwashe ′yan gudun hijira daga Tripoli | Labarai | DW | 25.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kwashe 'yan gudun hijira daga Tripoli

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta kwashe wasu 'yan gudun hijira na kasashe Afirka daga wani sansani a yankin Qasr Ben Gashir da ke kudancin Tripoli a kasar Libiya.

Hukumar ta ce ta yi hakan ne saboda kare rayukansu da lafiyarsu kasancewar yanayin tsaro a yankin ya tabarbare sakamakon rikicin da ke wakana tsakanin dakarun gwamnatin kasar da mayakan Khalifa Haftar.

Gabannin daukar wannan mataki dai, 'yan gudun hijirar wanda yawansu ya kai 325 kuma suka fito daga kasashen da suka hada da Najeriya da Sudan da kuma Eritrea sun gudanar da zanga-zanga kan halin da suke ciki, batun da ya janyo jikkatar 12 daga cikinsu.

Mukaddashin shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta MDD Matthew Brook ya ce 'yan gudun hijirar da ke Tripoli ba su taba fuskantar matsanancin yanayi kamar a wannan lokacin ba don haka ya zame musu wajibi su kwashesu daga inda suke don kaisu tudun na tsira.