An kwashe bakin hauren a Calais na Faransa | Labarai | DW | 26.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kwashe bakin hauren a Calais na Faransa

Mahukunta sun tabbatar dab kwashe daukacin bakin hauren da ke Calais na Faransa masu neman shiga Birtaniya.

An kwashe daukacin bakin haure da suka kafa sansani a tashar jiragen ruwan Calais da ke arewacin Faransa. Jami'an karamar hukumar sun ce haka ya biyo bayan gobarar da aka samu a sansanin bakin haure yayin da ake kwashe su zuwa wasu sassan kasar domin su neman mafaka ko kuma su koma kasashensu.

Fiye da mutane 5,000 suka yada zango a sansanin na Calais bisa tunanin watan-wata rana za su samu shiga Birtaniya ta barauniyar hanyar. Faransa ta nemi Birtaniya ta karbi daukacin yara da suke su kadai a sansanin, amma Birtaniya ta ce za ta amince da rabi.