An kori wasu sojojin rundunar MUNISCA | Labarai | DW | 12.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kori wasu sojojin rundunar MUNISCA

Majalisar Dinkin Duniya ta dauki matakin mayar da wasu sojojin Burundi uku da ke rundunar wanzar da zaman lafiyata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wato MUNISCA daga rundunar.

Kakakin ofishin da ke kula da aikin shirin zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniyar Ismini Palla wanda ya sanar a wannan Jumma'a da wannan mataki da Majalisar ta dauka ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa sun dauki matakin ne bayan da wani bincike da suka gudanar daga bisani ya gano cewa ana zargin sojojin uku da cin zarafin bil Adama da ake a kasarsu Burundi. Ya ci gaba da cewa mataki da suka dauka ya yi daidai da tanadin ka'idojin daukar ma'akata na Majalisar. Tuni dai Majalisar ta Dinkin Duniyar ta sanar da hukumomin Burundi da wannan mataki da ta dauka na korar sojojin kasar daga rundunar ta MUNISCA.