Wata kotu a Najeriya ta yi watsi da shari'ar mutanen nan 47 da ake zargi da aikata laifin neman jinsi guda a watannin baya, bayan da aka shafe tsawon lokaci ana shari'a kan batun a jihar Legas da ke kudancin kasar.
Da ya yanke hukunci, alkalin kotun ya ce rashin gabatar da cikakkun hujjoji a gaban kotun kan wadanda ake tuhuma ne ya sa ya yi watsi da karar. A bara ne ‘yan sanda suka yi dirar mikiya kan wani rukunin jama'ar da ke bikin zagayowar shekarar haihuwa tare da zargin su da laifin neman jinsi.
A shekarar 2014 ne dai karkashin gwamnatin Goodluck Jonathan, Najeriya ta kafa wata dokar da ke tisa keyar duk wanda aka sama da laifin aikata luwadi ko madigo a gidan yari har na tsawon shekaru 14.
Tuni dangi da ‘yan uwan wadanda aka tuhuma da aikata laifin suka jinjinawa matakin kotun na yau.