An kone wata budurwa a Bauchi | Labarai | DW | 01.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kone wata budurwa a Bauchi

Gungun wasu Matasa a garin Bauchi sun hallaka wata budurwa da ake zargi 'yar kunar bakin wake ce tare da koneta kurmus a lokacin da take kokarin shiga kasuwa.

A cewar sanarwar da kakakin 'yan sandar jihar ta Bauchi Haruna Mohammed ya karanta, wata budurwa ce da ba'a gano ko wacece ba, ta ki a binciketa yayin da tazo shiga cikin kasuwar Muda Lawal da ke Bauci, sai dai 'yan sanda sun tarwatsa gungun mutanen ba tare da sun kama kowa ba.

Shi ma dai wani mutun mai suna Safiyanu, da ya ganewa idanunsa yadda lamarin ya wakana, ya ce ita dai matar na tare ne da rakiyar wani namiji. Sai dai kuma hankalin mutane ya juya a kanta ne lokacin da taki a binciketa da na'urar bincike, sannan da aka daga hijabin da ke jikinta, sai aka gano wasu kwalabe guda biyu nannade da leda. Hakan ne ya janyo fushin al'umma suka far mata, kafin daga bisani su rataya mata wata tsofuwar taya tare da cinna mata wuta.