An koma tattaunawa kan rikicin Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 03.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An koma tattaunawa kan rikicin Sudan ta Kudu

Bangarorin da ke rikici da juna a Sudan ta Kudu sun koma teburin sulhu a kasar Habasha.

Bangarorin da ke rikici da juna na kasar Sudan ta Kudu sun koma teburin sulhu domin kawo karshen yakin basasan kasar na tsawon watanni 14, a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa kana madugun 'yan tawaye Riek Machar suna kokarin cimma matsaya ta karshe kafin wa'adin da shugabannin kasashen yankin suka yanke na ranar Alhamis.

Mai masaukin baki Firaminista Hailemariam Desalegn na kasar Habasha, ya ce babu lokaci mai yawa da ya rage wa bangarorin biyu da ke rikici da juna a kasar ta Sudan ta Kudu. Ana sa ran bangarorin su amince da matsaya domin kawo karshen yakin basasan da ya kai ga mutuwar dubban mutane, yayin da wasu fiye da miliyan guda suka tsere daga gidajensu.

A wanin labarin daukacin mambobin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da kakaba takunkumi kan duk wanda yake kawo tarnaki wajen samun zaman lafiya a Sudan ta Kudu.