An koma tattaunawa a kan Siriya a Geneva | Labarai | DW | 14.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An koma tattaunawa a kan Siriya a Geneva

Majalisar Ɗinkin Duniya da ke jagorancin taron za ta yi ƙoƙarin ganin an kawo ƙarshen yaƙin Siriya wanda aka kwashe shekaru shida ana yi.

Yau aka shirya za a sake komawa kan tebrin shawarwari a Geneva tsakanin gwamnati da 'yan tawayen Siriya a ƙarƙashin jagorancin MDD.Ƙasashen Faransa da Amirka sun yi kiran da a gudanar da sahihan shawarwari domin samar da zama lafiya a Siriya wacce ke fama da yaƙi kusan shekru shida da suka wucce.

Babban wakilin MDD da ke shiga tsakani a rikicin na Siriya Staffan de Mistura ya ce har a jiya bayan ya gana da wakilan gamatin da kuma na 'yan adawar akwai rashin fahimta juna wajen tsaida jadawalin bututuwan da a za a tattauna.