An koma tattaunawa a Geneve | Labarai | DW | 16.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An koma tattaunawa a Geneve

An sake komawa kan tebrin shawarwari tsakanin wakilan gwamnatin Siriya da na 'yan adawa a Geneve a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya .

Sabuwar tattaunawar wacce ba ta gaba da gaba ce ba, wacce mai shiga tsakanin na MDD Staffan de Mistura zai jagoranta. ita ce karo na biyar da ake yi da nufin kawo karshen yakin na Siriya da aka kwashe kusan shekaru shida ana yi ba tare da samun nasara ba. Sakamakon yadda dukkanin bangararon biyu da ke gaba da juna suka ki amincewa da tattaunawar gaba da gaba. Kawo yanzu  yakin na Siriya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu 320, yayin da wasu dubban jama'ar suka ficce daga matsugunansu.