An kira ′yan Turkiya su kauracewa Libya | Labarai | DW | 08.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kira 'yan Turkiya su kauracewa Libya

Wannan gargadi dai na zuwa ne bayan da Kamfanin sufirin jiragen sama na Turkish Airline ya bayyana daina zuwa wani yanki na kasar da ta shiga rudanin yaki.

Kasar ta Turkiya ta bukaci sauran 'yan kasarta da suka yi saura a Libya su gaggauta ficewa daga kasar saboda ci gaban tabarbarewar lamuran tsaro a kasar da yaki ya daidaita.

Mahukuntan kasar Turkiya sun kuma yi Allah wadai da wani kalami na da ake zargin cewa ya fito ne daga jami'an sojin saman kasar ta Libya, da ke cewa duk wani jirgin sama na fasinja ko na soja daga kasar ta Turkiya da ya yi yunkurin bi ta samaniyar ta Libya ana iya harbo shi. Abinda mahukuntan na Turkiya a yau Laraba ke cewa abu ne da ba zasu lamunta kuma abu ne da bai daceba.

A cewar ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Turkiya duk mutanen kasar da suka yi saura a kasar ta Libya su gaggauta ficewa dan gudun abin da ka iya zuwa ya dawo saboda yanayin da kasar ke ciki.

Wannan gargadi dai na zuwa ne bayan da Kamfanin sufirin jiragen sama na Turkish Airline ya bayyana cikin makonnan cewa ya tsaida zirga-zirgarsa zuwa birnin Tripoli.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu