1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Zaben Isra'ila karkashin matakan coronavirus

Suleiman Babayo
December 23, 2020

Masu zaben Isra'ila za su sake komawa runfana bayan an kira sabon zabe karo na hudu a kasa da shekaru biyu.

https://p.dw.com/p/3nAVA
Israel | Premierminister Netanjahu Rede Knesset Likud
Hoto: Yonatan Sindel/REUTERS

Masu zabe a Isra'ila za su sake komawa runfunar kada kuri'a karo na hudu cikin kasa da shekaru biyu, yayin da Firaminista Benjamin Netanyahu yake shirin fuskantar tuhuma kan cin hanci, zargin da ya musanta.

Zaben wanda aka tsara a watan Maris na sabuwar shekara ta 2021, za a gudanar saboda rashin cimma matsaya kan kasafin kudi a majhalisar dokoki a wannan Talata da ta gabata duk da matakan da ake dauka na hana yaduwar annobar cutar coronavirus, lamarin da ya zama sabon kalubale ga Firamnista Benjamin Netanyahu wanda ya fi kowa dadewa kan mukamun tun da aka kafa Isra'ila, inda jam'iyyarsa ta Likud ke rike da madafun iko tun shekara ta 2009, lokacin da ya sake dawowa karagar mulki.

Shi dai Netanyahu dan shekaru 71 da haihuwa ya fara rike mukamun daga shekarar 1996 zuwa shekarar 1999.