An kawo karshen wani hari da Taliban ta kai kan ginin majalisar dokokin Afghanistan | Labarai | DW | 22.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kawo karshen wani hari da Taliban ta kai kan ginin majalisar dokokin Afghanistan

An kashe dukkan mutane bakwai da suka kai harin kan majalisar dokokin ta Afghanistan da ke birnin Kabul.

An murkushe wani hari da mayakan kungiyar Taliban suka kai kan ginin majalisar dokokin Afghanistan da ke birnin Kabul. Kakakin ma'aikatar cikin gida ya ce an kashe dukkan mutane bakwan da suka kai harin. Da farko wani dan kunar bakin wake ya ta da bam a cikin wata mota kusa da ginin sannan dakarun tsaro sun kashe sauran abokan tafiyarsa. Akalla mutane 31 sun samu raunuka a harin. An kai harin ne lokacin bikin ransar da sabon ministan tsaro Mazum Staniksai. An ji karan harbe-harbe da tashin bama-bamai a kusa da ginin majalisar dokokin.