An kashe Yazidawa kimanin 100 a Iraki | Labarai | DW | 16.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe Yazidawa kimanin 100 a Iraki

Rahotannin da ke shigo mana daga Iraki na cewar masu fafutuka ta kafa daular Musulunci karkashin kungiyar nan ta IS a Iraki sun kashe Yazidawa da dama.

Jami'an gwamnati Iraki sun ce wanda suka tsira da rayukansu a irin hare-haren da masu kaifin kishin addini na kungiyar nan ta IS a Iraki suka kai kauyukan da Yazidawa ke zaune sun shaida musu cewar masu fafufutar sun kashe sama da mutane 100.

Guda daga cikin jami'an da suka shaida wannan labarin suka ce 'yan IS sun yi wa kauyen Kocho tsinke ne a 'yan kawankin da suka gabata inda suka yi ta tilastawa mutanen garin shiga addinin Isama, yayin da a hannu guda suka yi garkuwa da mata da kananan yara.

Jami'an sun ce kisan mutanen ya faru ne a jiya Juma'a a kauyen wanda tuni ya rigaya ya fada hannun 'yan IS to sai da babu wata kafa mai zaman kanta da ba ta gwamanti ba da tabbatar da wannan labarin.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar