1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan shekaru 13 ya hallaka Yahudawa bakwai

Ramatu Garba Baba
January 28, 2023

Wani Bafalasdine ya bude wuta a kusa da wurin bautar Yahudawa inda nan take ya hallaka mutum akalla bakwai tare da raunata wasu mutum uku.

https://p.dw.com/p/4Mor3
Hoto: Reuters/R. Zvulun

Binciken farko ya tabbatar da cewa, Bafalasdinen da ya bude wuta a daf da wani ginin bautar Yahudawa, dan shekaru goma sha uku ne da haihuwa, harin da Isra'ila ta ce shi ne mafi muni da ta gani a shekarun baya-bayan nan, ya hallaka mutum akalla bakwai tare da raunata wasu uku, kafin daga bisani yan sanda su harbe matashin har lahira. Daga cikin wadanda suka gamu da ajalinsu a kazamin harin na daren Jumma'ar da ta gabata, har da wata dattijuwa 'yar shekaru saba'in.

Harin dan bindigan na zuwa ne a yayin da ake zaman dar-dar bayan wani samame da sojojin Isra'ilan suka kai kan wani sansanin 'yan gudun hijira da ke yankin Jenin a Gabar Yamma da Kogin Jordan a ranar Alhamis da ta gabata inda mutane tara suka rasa rayukansu. Isra'ila ta ce, ta kai harin ne da zummar dakile wani gagarumin hari na ta'addanci.