An kashe wata tsohuwar minista a Burundi | Labarai | DW | 14.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wata tsohuwar minista a Burundi

'Yan sanda a Burundi sun sanar da cewar an kashe wata tsohuwar ministan Hafsa Mossi ta kusa da shugaba Pierre Nkurunziza.

Hafsa 'yar majalisar dokoki ta kasashen kungiyar gabashin Afirka kana 'yar jam'iyyar da ke yin mulki. Wasu 'yan bindiga ne guda biyu cikin mota a wata unguwar da ke a gabashin Bujumbura babban birnin kasar suka harbeta har lahira.

Tun lokacin da aka fara tashin hankalin na Burundi a shekara bara, mayan sojoji da dama aka kashe saboda ra'ayinsu na goyon bayan shugaba Pierre Nkurunziza wanda ya yi tazarce a karshen wa'adin mulkinsa.