An kashe wasu jami′an Hukumar PAM | Labarai | DW | 15.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wasu jami'an Hukumar PAM

An ba da rahoton cewar an kashe wasu jam'ian hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya guda uku PAM a Sudan ta Kudu.

Mutanen sun gamu da ajalinsu ne a kan hanyarsu ta zuwa wajen wani rumbun tsimi na hukumar inda suke yin aikin rarraba abinci. A sa'ilin da wani fadan da aka gwabza a garin Wau da ke a yankin arewa maso gabashin kasar tsakanin dakarun da ke yin biyayya ga shugaba Salva Kiir da kuma na tsohon mataimakinsa Riek Mashar ya rutsa da su. Ma'aikatan na PAM wadanda dukkaninisu guda uku 'yan Sudan ta Kudu ne, biyu an datsesu da ada, yayin da daya aka harbeshi har lahira.