An kashe wani jagoran Al-Qaida a Yemen | Labarai | DW | 08.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wani jagoran Al-Qaida a Yemen

Wata cibiyar tsaro ta Amirka ta ba da sanarwa kashe Nasser bin Ali al-Ansi

Cibiyar ta ce an kashe wani babban jam'in Ƙungiyar Al-Qaida na ƙasashen yankin Larabawa a Yemen.Jagoran cibiyar ta AQPA wanda ya bayyana sanarwa jiya. Ya ce an kasheshi a cikin wasu hare-hare na jiragen sama na yaƙi marasa matuƙa da Amirka ta kai a garin Mukalla da ke cikin lardin Hadramut na Yemen a cikin watan da ya gabata.

Nasser bin Ali al-Ansi shi ne ya yi iƙirarin kai hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar 'yan jaridar nan na Faransa na Charli Hebdo.