An kashe wani babban jam′in tsaro a Libiya | Labarai | DW | 12.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe wani babban jam'in tsaro a Libiya

Rahotanni daga Tripoli babban birnin Libiya, sun ce wasu mutane sun hallaka babban Daraktan 'yan sandar ƙasar bayan da suka buɗe masa wuta.

Kisan ya faru ne wannan Talatar(12.08.2014) inda wasu mutane masu fuskoki a rufe, suka buɗe wuta ga motar Kanal Mohamed al-Souissi.

Wanda ke kan hanyarsa ta dawowa gida daga birnin Tajoura da ke gabashin Tripoli, inda ya halarci zaman taron Majalisar wannan ƙaramar hukumar a cewar wata majiyar jami'an tsaro. Daraktan 'yan sandar ya rasu ne lokaci kaɗan bayan da aka isa da shi zuwa wani asibiti mafi kusa, kuma babu wasu da suka ɗauki alhakin kai wannan hari yazuwa yanzu

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane