An kashe sojoji biyar a Juba | Labarai | DW | 05.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe sojoji biyar a Juba

Rundunar sojin kasar Sudan ta Kudu ta nunar da cewar, an samu lafawar lamura bayan wannan rikici da ke da nasaba da rashin samun albashin sojojin na watanni uku.

A kalla sojoji guda biyar ne suka rasa rayukansu, a wani fada da ya barke a barikin soji da ke birnin Juba, wanda aka danganta da sabani kan jinkirta biyan albashinsu. Kakakin rundunar ya shaidar da cewar, fada makamancin wannan a watanni uku da suka gabata, ya fadada zuwa wasu yankuna. Sai dai acewarsa, yanzu an samu lafawar lamura. Wannan rikici dai bashi da nasaba da 'yan tawaye, sai dai kamar na baya da ya kusan jefa wannan jaririyar kasar Afrika cikin yakin basasa, kafin a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 23 ga watan janairun da ya gabata. Kungiyar hadakar kasashen yankin ta IGAD dai, ta kasance mai shiga tsakani a kokarin warware rikicin, inda har yanzu ba'a fara tattaunawar sulhu ba.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Auwal Balarabe