An kashe maharin birnin Barcelona | Labarai | DW | 21.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe maharin birnin Barcelona

'Yan sanda a kasar Spain sun tabbatar da labarin harbe mutumin da ya kai hari a wani dandalin shakatawa a birnin Barcelona da ya salwantar da rayuka 13.

'Yan sanda a kasar Spain sun tabbatar da labarin harbe mutumin da ya kai hari a wani dandalin shakatawa a birnin Barcelona, inda rayukan mutane 13 suka salwanta, 'yan sanda sun ce sun harbe maharin mai suna Younes Abuyaqoub a garin Subirats da ke yammancin birnin na Barcelona a yau Litinin, an kaddamar da samame a kauyen da Abuyaqoub ya buya bayan an kwarmata wa jami'an tsaro.

Sanarwar ma'aikatar tsaron ta ce maharin ya na sanye da jigidar bama-bamai a lokacin artabun da ya yi sanadiyar mutuwarsa sai dai daga bisani 'yan sanda sun gano cewar jigidar ta bogi ce, Abu Yaqoub mai shekaru 22 dan asalin kasar Moroko ne mai takarda izinin zama a Spain, al'amarin ya kawo karshen farautar da aka kwashi kwanaki a na yi a harin makon da ya gabata da ya matukar girgiza al'ummar kasar.