An kashe kwamandan Al Shabaab | Labarai | DW | 01.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe kwamandan Al Shabaab

Rahotanni daga Somaliya na cewa an kashe wani kwamandan mayakan Al Shabaab lokacin wani sumame da dakarun gwamnati suka kai yankin kudancin kasar.

A cewar hukumomin kasar ta Somaliya cikin wata sanarwa, an kashe zarton na Al Shabaab ne a wani harin da wani jirgi maras matuki ya kai wa mayakan na tawaye. Ma'aikatar watsa labaran kasar, ta ce ta yi amannar cewa babban mayakin na Al Shabaab da aka halaka, shi ne a baya ya sha kitsa munanan hare-haren da suka salwantar tare da jikkata jama'a a Mogadishu babban birnin Somaliyar.

Gwamnatin Somaliya dai na ganin mutuwar kusan na iya matukar rage karfin kungiyar a kasar da ma sauran kasashe irinsu Kenya da Uganda da suke aikata aika-aika a ciki.

Kungiyar ta Al Shabaab dai ba ta yi wani martani dangane da sanarwar gwamnatin ta Somaliya ba.