An karfafa matakan tsaro a wajen bikin yan shi′a | Labarai | DW | 09.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An karfafa matakan tsaro a wajen bikin yan shi'a

An karfafa matakan tsaro a birnin Bagadaza yayinda dubban yan shia suke gudanar da ziyarar ibada a babban birnin kasar ta Iraqi.

Shekaru biyu da suka shige kusan masu ziyara 1,000 ne suka rasa rayukansu cikin yamutsi daya barke kann wata gada kusa da kabarin Imam Musa Khadim yake bayan an firgita mutane game da wani dan kunar bakin wake da aka ce yana tsakaninsu.

A jiya laraba dakarun da Amurka ke jagoranta sun sanarda kashe wasu mutane 30 a birnin Sadr na yan shia,hakazalika rundunar sojin Amurka ta sanarda mutuwar wasu sojojinta uku wasu kuma hudun suka samu rauni cikin saoi 24 a Iraqi.Yayinda kuma sojojin Burtaniya 2 suma suka halaka a safiyar yau din nan a yammacin Bagadaza,wanda hakan ya kawo yawan sojojin Burtnaiya zuwa 4 da suka rasa rayukansu cikin saoi 48.