1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Kristoci ta nemi sulhunta rikicin Kamaru

Lateefa Mustapha Ja'afar RGB
November 30, 2018

Kungiyar Kiristoci ta AGC na yankin da ke magana da turancin Ingilishi ce ta gudanar da wani taro a garin Buea da nufin lalubo hanyar da za a bi wajen kawo karshen rikicin da yankin ke fama da shi.

https://p.dw.com/p/39EEu
Karte Kamerun Mamfe Bamenda Buea ENG

Masu shirya wannan taraon dai sun bayyana shi a matsayin matakin farko na kawo karshen rikicin da ya dabaibaye yankin Arewa maso Yamma da kuma Kudu maso Yammacin kasar ta Kamaru. Sun kuma yin kira ga mahukuntan Yaounde da su bayar da sanarwa a hukumance da ke nuni da yadda gawamnati ke goyon bayan taron wanzar da zaman lafiyar.

Taron wanda aka gudanar a karkashin jagorancin Archbishop na Douala, Cardinal Tumi ya samu halartar wakilin Baptis na Kamarun Rev. Timothy Limbe da sauran malaman addinai. Yayin da masu shiga tsakani suka sha alwashin gudanar da shi ba tare da nuna bangaranci ba, Cardinal Tumi da wasu da suka shirya taron, sun bukaci dukkanin bangarorin da su yi kokarin tabbatar da sulhun.

 

Yayin taron da aka gudanar a karon farko a garin Buea da ke zaman fadar gwamnatin gundumar Kudu maso Yammacin Kamarun, masu shirya taron sun jaddada aniyarsu ta gudanar da shi ba tare da nuna bangaranci ba.Babu dai tabbacin lokacin da za a sake shirya wannan taron, sai dai kungiyar Kiristocin ta yankin masu magana da Turancin Ingilishin, ta ce tana fatan ya kasance nan ba da jimawa ba.