An kame daruruwan masu zanga-zanga a Moscow | Labarai | DW | 27.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kame daruruwan masu zanga-zanga a Moscow

A kasar Rasha 'yan sanda sun kame mutane kimanin da 650 a lokacin wata zanga-zanga da 'yan kasar suka shirya a wannan Asabar a birnin Moscow domin neman a shirya zabukan gama gari a kasar. 

Dubunnan jama'a ne dai suka fantsama a saman babban titin tsakiyar birnin na Moscow suna ta furta kalaman batanci ga mahukuntan Kremlin da kuma kira ga a shirya zabuka gama gari da kuma bai wa duk mai 'yanci tsayar da takararsa.

 'Yan sanda sun yi amfani da karfin tuwo wajen tarwatsa zanga-zangar da aka nemi shiryawa a gaban harabar ma'aikatar magajin garin birnin na Moscow ba tare da izinin hukuma ba. 

Da ma dai tun kafin soma zanga-zangar a wanann Asabar 'yan sanda sun kame jagorin 'yan adawa da dama  kafin sako su daga bisani bayan cin wasunsu tarar kudi. Wannan na zuwa ne kasa da mako daya da shirya wata kasaitacciyar zanga-zangar da jama'a suka shirya a birnin na Moscow