1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa: An cafke Ahmad Ahmad na CAF

Abdul-raheem Hassan
June 6, 2019

Hukumomin bincike a kasar Faransa sun tsare shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka Ahmad Ahmad kan zargin cin hanci da wadaka da kudin hukumar.

https://p.dw.com/p/3JzZS
Ahmad Ahmad
Hoto: Getty Images/AFP/Rijasolo

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA dai, ta ce ba da masaniya kan laifin da ake tuhumar Ahmad Ahmad da shi, amma ta bukaci karin bayani daga masu binciken a Faransa. Wata jaridar Afirka, Jeune Afrique ce da fara yada labarin inda ta ce an kama Ahmad Ahmad dan kasar Madagaska kan zargin cin hanci a hukumar ta CAF, bayan da tsohohon sakatare janar na hukumar ya zargi Ahmad din da bai wa shugabannin kungiyoyn kwallon kafa cin hanci domin yin sama da fadi da dubban daloli. An kama shugaban CAF din ne, kwana guda gabannin fara gasar cin kofin duniya na mata na 2019 a kasar ta Faransa.