1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan- Uba ya harbe jaririyarsa har lahira

Ramatu Garba Baba
March 10, 2022

Jami'an 'yan sanda sun yi nasarar cafke mutumin da ya kashe jaririyarsa saboda kin jinin 'ya mace. Shahzeb Khan ya jima yana son ya haifi da namiji da zai zama magajinsa.

https://p.dw.com/p/48JlQ
Pakistan | Anschlag in Lahore
Hoto: K.M. Chaudary/AP Photo/picture alliance

Yan sanda a kasar Pakistan sun ce, sun yi nasarar kama mutumin da ya kashe jaririyarsa a makon jiya, Shahzeb Khan da ke zaune a yankin Punjabi, ya harbi jaririyar har sau biyar kuma ta mutu nan take. Mai dakinsa ta sheda cewa, Mista Khan ya fusata da haihuwar 'ya mace a maimakon samun da magaji namiji da ya jima yana fatan samu.

Kisan jaririyar ya tayar da hankula da rudani da kuma tofin Allah-wadai daga jama'a, daga bisani da taimakon jami'an tsaro da kuma hadin kan jama'ar gari aka yi nasarar cafke mutumin da ya arce da gudu bayan aikata kisan, an kwashi kwanaki ana farautarsa kafin ya shiga hannun hukuma. Maza da dama a  Pakistan sun fi son haihuwar yara maza fiye da mata.