An kama masu yunkurin juyin mulkin Burundi | Labarai | DW | 15.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama masu yunkurin juyin mulkin Burundi

Jami'an tsaron da ke biyeyya ga Shugaba Pierre Nkurunziz, sun kama manyan sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki a Bujumbura bayan da suka mika kansu dakansu.

Yayin da yake magana ta wayar tarho da kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP Janar Niyombare ya ce sun amince su mika kansu inda ya ce sun kira ministan cikin gidan kasar da ma na tsaro inda suka sanar da su cewa basa dauke da makamai.

Tun dai a jiya ne janar Cyrille Ndayirukiye da ke a matsayin na hannun damar janar Niyombare, ya sanar cewa yunkurin nasu ya ci tura ganin yadda suka fuskanci jajircewa daga sojoji masu kare wannan gwamnati. Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Bam Ki Moon ya yi Allah wadai da yunkurin juyin mulkin inda ya yi kira da a dawo da kwanciyar hankali a wannan kasa.