An kama abin hada nakiya a gidan maharan Barcelona | Labarai | DW | 20.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama abin hada nakiya a gidan maharan Barcelona

Jami'ai a Kataloniya sun ce sun sami sama da zungurun iskar gas 120 da ake zargin kayayyakin hada bama-bamai ne a daya daga cikin gidajen wadanda suka kai harin Barcelona ke zaune.

'Yan sandan Kataloniya sun ce sun sami sama da zungurun iskar gas 120 da ake zargin kayayyakin hada bama-bamai ne a daya daga cikin gidajen wadanda suka kai harin Barcelona suka zauna a ciki. An kuma hakkake cewa kayayyakin na gidan ne watanni shida da suka gabata.

'Yan sanda sun kuma ce kwararrun masu bincike na ci gaba da aiki kan mutane 12 da ake zarginsu da harin, yayin kuma da a daya bangaren ake ci gaba da neman wani dan Moroko ne Younus Abou Yakoub mai shekaru 22 da kawo i yanzu ba a san inda ya labe ba.

A shari guda kuwa a yau Lahadi ne aka yi addu'o'i na musamman saboda wadanda suka mutu a harin na Barcelona su 14. Sarki Felipe da Gimbiya Letizia da ma Firaminista Mariano Rajoy sun halarci taron na addu'o'i.