1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amrullah Saleh ya tsallake harin ta'addanci

Binta Aliyu Zurmi MNA
September 9, 2020

Wata mota shake da bama-bamai ta tashi da ayarin motocin mataimakin shugban kasar Afganistan Amrullah Saleh a kan hanyarsa ta zuwa aiki ta halaka mutane da dama.

https://p.dw.com/p/3iC5E
Afghanistan Vize-Präsident Amrullah Saleh
Hoto: picture-alliance/AP/R. Gul

Mataimakin shugaban  Afganistan Amrullah Saleh ya tsallake rijiya da baya amma an sami mutuwar mutum biyu tare da jikkatar wasu 12 daga cikin jami'an tsaronsa da sanyin safiyar wannan Laraba.

Har wayau an sami mutuwar fararen hula sama da 20 sannan wasu kimanin 50 sun jikkata a wajen da lamarin ya auku a cewar ma'aikatar lafiyar kasar. 

Ya zuwa wannan lokacin babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari. Amma dai ana zargin 'yan kungiyar Taliban kasancewar Amrullah Saleh ya dade yana sukar lamirin ayyukan 'yan kungiyar.

Wannan harin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake dakon ci gaba da zaman sulhu da 'yan Taliban a birnin Doha na kasar Qatar.

Haka kuma a wannan Laraba shugaban Amirka Donald Trump ke shirin sanar da janye dakarun sojin kasarsa daga Afganistan kamar yadda yarjejeniyar da suka cimma da 'yan Taliban ta tanada.