An kai harin kunar bakin wake a Gombe | Labarai | DW | 01.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai harin kunar bakin wake a Gombe

Wani dan bindiga ya rasa ransa bayan da bam dake jikinsa ya tarwatse a wajen wata majami'a da ke Gombe a lokacin gudanar da ibada ta shiga sabuwar shekara ta 2015.

Masu aiko da rahotanni suka ce bam din ya tashi ne lokacin da 'yan agaji a majami'ar suka yi kokarin tankwarashi ya ajiye babur dinsa inda aka kebe, umarnin da dan kunar bakin waken ya yi yunkurin kin amincewa da shi.

Shugaban hukumar bada gaji gaggawa ta Red Cross a Gombe Abubakar Yakubu ya ce babu asarar rai da ka samu bayan ta maharin. Sai dai wasu mutanen da ba su da yawa sun samu kananan raunuka.

Wata mata da abin ya faru kan idonta ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar ta ga an fita da wasu 'yan mata jina-jina daga cikin cocin don kaisu asibiti.