An kai harin bam a wajen taron tuni da yakin duniya na biyu | Labarai | DW | 11.11.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai harin bam a wajen taron tuni da yakin duniya na biyu

Mutane da dama aka tabbatar sun ji rauni a sakamakon harin bam da wasu da ba a san ko su waye ba suka kai a yayin wani bikin tuni da wadanda suka rasa rayukansu a lokacin yakin duniya na daya.

A birnin Jeddah na kasar Saudiyya, mutane da dama sun ji rauni bayan wani harin bam da aka kai kan wani taron jama'a da ke halarta bikin tuni da wadanda suka rasa rayukansu a yakin duniya na daya. Mahalartar taron da aka yi a wata makanbarta, sun hada da wakilan ofisoshin jakadanci na wasu kasashen Turai, ciki har da Faransa, a lokacin da aka kai harin da safiyar wannan Laraba.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Faransan ta fitar ta soki manufar kai harin tare da yin alla-wadai. Babu dai cikakken bayani dangane da batun daga mahukuntan kasar ta Saudiyya kan alkaluman wadanda harin ya rusta da su kawo yanzu. Tuni aka karfafa matakan tsaro a duk sassan kasar.