An kai harin bam a masallacin Jumma′a a Kano | Labarai | DW | 28.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai harin bam a masallacin Jumma'a a Kano

Rahotanni daga birnin Kano na arewacin Tarayyar Najeriya na cewa, wani bam ya fashe a masallacin Sarki da ke birnin na Kano yayin da dubban mutane suka hallara domin sallar Jumma'a.

A dazu-dazun nan ne, wani bam ya fashe a babban masallacin Juma'a da ke birnin Kano a Tarayyar Najeriya da aka fi sani da Masallacin Sarki, ya yin da dubban mutane suka hallara domin gudanar da Sallar Jumma'a. Sai dai har kawo yanzu babu wani adadi da aka bayar na wadanda suka rasu ko suka jikkata sakamakon harin. Masallacin dai da ke tsakiyar birnin na Kano shi ne Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu yake yin limanci a cikinsa a duk ranakun Jumma'a. Wannan dai na zaman hari mafi muni da aka kai a masallaci a birnin na Kano, ko da yake dama an taba samun wani da ya yi yunkurin kai hari a wannan masallacin a shekarar da ta gabata, sai dai bai kai ga cimma nasara ba.

Mawallafi: Salissou Boukari

Edita : Mohammad Nasiru Awal