An kai hari sansanin ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 29.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari sansanin 'yan gudun hijira

Mutane 4 ciki har da maharan ne suka mutu a harin bam da aka kai a sansanin 'yan gudun hijira da ke a jahar Diffa ta Jamhuriyar Nijar

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da cewa wasu mata guda biyu 'yan kunar bakin wake sun kai hari cikin sansanin 'yan gudun hijira mafi girma da ke a Kabalewa na jihar Diffa inda suka tayar da bama- baman da ya yi sanadiyar rayukan mutane biyu tare da raunata wasu mutane goma sha daya. Matan ma dai sun tarwatse a harin da suka kai a daren Laraba.

Tuni dai aka kwashe wadanda suka sami rauni zuwa asibiti don ba su kulawa. Ana kuma zargin matan 'yan kungiyar Boko Haram ne. Sansanin da aka kai harin dai yana da girman gaske inda ake tsugune da daruruwan mutanen da rikicin Boko Haram ya daidaita.