An kai hari kan musulmi a New Zealand
March 15, 2019Talla
Mutumin da aka ce ya kutsa masallacin al Nuri lokacin sallar Juma'a, sanye da bakaken kaya, ya buda wutar ne da wata bindiga mai sarrafa kanta, inda kuma ya kashe akalla mutum na akalla mutum 40.
Shaidu sun ce mutumin da ya kai harin ya sanya hular kwano da ke daukar naurar daukar hoton da ta watsa kai tsaye ta kafar sadarwar Intanet.
'Yan sanda sun gargadi jama'a da a guji yada hotunan harin ta shafukan sada zumunta, saboda muninsu. Galibin wadanda ke masallacin dai baki ne da suka fito daga wasu kasashe.
Firaministar New Zealand, Jacinda Ardern, ta bayyana harin da cewa na ta'addanci ne.
Ana kuma tsare da mutane hudu da suka hada da wani dan kasar Ostireliya da kuma wata mace guda.