An kai hari kan mayaka a yammacin Tripoli na Libiya | Labarai | DW | 15.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari kan mayaka a yammacin Tripoli na Libiya

Wani jirgin yaki da ba a tantace ba, ya kai hari kan wani barakin soja da ke hannun mayaka masu adawa da gwamnati a yankin Gharyan da ke yammacin kasar.

A cewar kamfanin dillancin labaran kasar ta Libiya, Lana, harin dai ya taba wani wurin ajiye makammai da ke hannun mayakan a birnin Gharyan da ke a nisan kilomita 120 a kudu maso yammacin birnin Tripoli. Harin ya kuma haddasa jikkatar mutane da dama, yayin daga nashi bangare gidan Telebijin din Al-Nabaa ya sanar cewa mutane akalla 11 sun ji rauni.

Su dai wadannan mayaka na Gharyan, na daga cikin gungun mayakan Fajr Libiya, wata kungiya da ta kumshi kabilu daban-daban na kasar, wadanda suka yi nasarar karbe iko a birnin Tripoli a watan August da ya gabata, bayan da suka fatattaki mayakan Zenten da ke rike da filin jirgin saman birnini.