SiyasaAfirka
An kai hari filin jiragen sama na Khartoum
October 21, 2025
Talla
Harin na zuwa a daidai lokacin da ake kokarin sake bude filin jiragen saman domin ci gaba da gudanar da zirga-zirgar cikin gida tun bayan shekaru biyu da rufe shi, sakamakon yakin da ake gwabazawa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun rundunar kar-ta-kwana ta RSF.
Karin bayani: Mayakan RSF sun kai hari Port Sudan
Shaidun gani da ido sun bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa sun ji karar tashin bama-bamai sakamakon hare-haren jirage marasa matuka a yankin tsakiya da kuma kudancin birnin Khartoum da ke daura da filin jirgin babban birnin.