An kai hari a wata makaranta a Faransa | Labarai | DW | 16.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari a wata makaranta a Faransa

Ba a dai kai ga fayyace cikakkun bayanai kan maharin ba. Sai dai wasu bayanai na nuni da cewa dalibai ne guda biyu suka bude wuta a kan shugaban makaranta.

Akalla mutane uku suka samu raunika bayan harbi da bindiga a wata babbar makaranta a wani karamin gari mai suna Grasse da ke a Kudancin Faransa, kawo yanzu dai maharin da ke zama wani matashi dan shekaru 17 dauke da bindigogi da makamin gurneti an cafke shi kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gidan Faransa da ma 'yan sanda suka bayyana.

Ba a dai kai ga fayyace cikakkun bayanai kan maharin ba. Sai dai wasu bayanai na nuni da cewa dalibai ne guda biyu suka bude wuta a kan shugaban makarantar wanda kawo yanzu ke cikin mutanen da suka sami raunika. Babu dai bayanai kawo yanzu ko maharan su na da alaka da ta'addanci.

Daya dai cikin maharan da ake zargi na hannun jami'n tsaro, yayin da dayan ya tsere. Wani ganau kan abin da ya faru ya ce dalibai sun gudu sun dauki mafaka a wani babban shagon cefane da ke kusa da makarantar.