An kai hari a Nairobi | Labarai | DW | 11.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kai hari a Nairobi

Wani bam ya fashe a wajen wani gidan cin abinci a tsakiyar birnin Niarobi na kasar Kenya inda akalla mutune2 guda ya halaka wasu kuma 30 suka samu raunuka.

Komishinan yan sanda Manjo janar Hussein Ali ya tabbatar da cewa mutum guda ya rasa ransa wasu kuma 6 sun samu rauni,amma kuma yaki cewa komai game da harin.

Kasar Kenya dai tana cikin shirin kota kwana tun watan janairu lokacinda gwamnati ta zargi wasu mayakan islama da suka tsere daga kasar Somalia.