1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari a masallacin Afghanistan

August 3, 2018

Mutane da dama sun salwanta yayin da wasu ma sun jikkata a wani hari da aka kaddamar a masallacin 'yan Shi'a a Afghanistan.

https://p.dw.com/p/32aeJ
Afghanistan, Selbstmordangriff in Gardez
Hoto: picture-alliance/Ahmadi

Rahotannin da ke fitowa daga kasar Afghanistan, na cewa akalla mutane 25 ne suka sun salwanta, yayin da wasu 56 kuwa suka jikkata a wani hari da aka kaddamar a wani masallacin 'yan Shi'a da ke a gabashin kasar.

Harin wanda na kunar bakin wake ne da wasu mutanen biyu suka kai, ya faru ne a birnin Gardiz, kamar dai yadda hukumomi suka tabbatar.

Harin wanda ya zuwa yanzu, ba bu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai shi, an kaddamar da shi ne lokacin da masallata ke sallar Juma'a a masallacin.

A share guda kuwa, wata majiya ta rundunar jami'an 'yan sanda da ke lardin Paktiya, ta ce alkaluman wadanda suka mutu da ma suka jikkata, mutum 20 ne.